Sports
Italiya ta bukaci a mika mata tsohon dan wasan kwallon kafa Robinho don fuskantar Shari’a
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Ma’aikatar shari’a ta Italiya ta bukaci a mika mata tsohon dan wasan kwallon kafa Robinho daga Brazil, kamar yadda kakakin ma’aikatar ya bayyana a yau Talata.
Ofishin mai gabatar da kara ne ya gabatar da bukatar a watan Fabrairu kuma yanzu an tura buƙatar a hukumance ga hukumomin Brazil.
’Yan Yahoo-Yahoo Sun Yi Bore Kan Kamen EFCC
An yanke wa tsohon dan wasan AC Milan hukuncin daurin shekaru tara a gidan yari a Italiya saboda zarginsa da yi wa wata mata fyade a wani wurin shakatawa, tare da wasu maza biyar a shekarar 2013.
Robinho, wanda ya lashe kofin Copa America a shekarar 2007 da Brazil, ya musanta zargin.
Sai dai mai yiwuwa ɗan shekaru 38 ɗin ba zai yi zaman gidan yarin a Italiya ba, saboda ba a yarda Brazil ta mika ‘yan kasarta kamar yadda kundin tsarin mulkinta ya tanada ba.
Za a iya kama Robinho ne kawai idan ya yi balaguro zuwa ƙasashen waje kuma umarnin kama shi na ƙasa da ƙasa zai fara aiki.
A watan Oktoba na 2020, Robinho ya so ya dawo ƙwallon ƙafa tare da kungiyar kwallon kafar Santos na garinsu, amma saboda matsin lamba daga masu tallafawa da magoya bayansa saboda hukuncin da aka yanke masa, sai a ka katse kwantaragin, inda daga bisani sai ya yi ritaya daga kwallon kafa.
