News
Dubban ƴan Kwankwasiyya sun tarbi Kwankwaso domin buɗe ofishin NNPP a Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Dubban ƴan Kwankwasiyya ne su ka yi dafifi domin tarbar da kuma gane wa idonsu buɗe ofishin jam’iyyar adawa ta NNPP da ɗan takarar ta na shugabancin ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso zai yi a jihar Kano a yau Lahadi.
TSARO: Gwamnatin Neja Ta Rufe Makarantun Firamare Da Sakandare
INDARANKA ta jiyo cewa yanzu haka magoya baya sun dafifi su na tsimayen tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP domin buɗe ofishin a unguwar Sharada da ke birnin Kano.
Wannan jarida ta jiyo cewa tuni dai gurin ya rincaɓe da magoya baya, babu masakar tsinke, inda hakan ya haifar da cunkoson ababen-hawa a yankin da ma titunan da su kai haɗaka da Sharada.
Ƙarin bayani na nan tafe…
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
