News
Zaben 2023 :Kalubale ga matasan Nigeria a zaben shekarar 2023
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kamar yadda Jama,a ke cewa matasa sune kashen bayan kowacce Al,umma a duniya.
A dai,dai lokacin da zaben shekarar 2023 ya rage saura watanni uku da Yan kwanaki a Nigeria masana na ganin cewa akwai mahimmiyar gudunmawar da matasa zasu iya bayarwa wajan samar da shugaba nagari.
Jerin ’Yan Kwallo 10 Da Suka Samu Kudi Mai Tsoka A 2022
Saidai a Nigerer a iya cewa da sauran runa a kaba domin kuwa da su matasan ake yin Wani abun da ba dai,dai ba musamman a lokutan Zabe domin kuwa wasu Yan siyasa suna amfani da matasa wajen cimmma burikansu ko muradinsu
Ana samun wasu Yan siyasa suna amfani da karfin da matasa ke dashi wajen Basu abubuwan da bai kamataba wajen yin bangar siyasa musamman a lokacin zabe domin kuwa anabasu makamai domin suyu sare,sare da yanke yanke Wani lokacin ma har da kisan Kai
Saidai Kuma hukumar Zabe Mai zaman kanta ta kasa INEC ta,ce tana um
Umartar duk wasu Yan siyasa da su guji tada zaune tsaye a lokacin zabe domin gojewa fadace fada,ce domin cewar,ta duk Wani Dan siyasa da aka samu ya karya doka to ko shakka babu zai fuskanci hukuncin shariar inji INEC
Wasu matasa da Jaridar Indaranka ta tattauna dasu sunce ai su yanzu sun Gane gaskiya domin kuwa a zaben an shasu sun warke domin kuwa bazasuyi abunda bai dace dasu ba Kuma baza suyi Wani aikin da ya sabo da dokaba sunkara da cewa sunajin karattukan malamai daban daban akan irin wannan matsalar
Wani malami da ya bukaci mu sakaye sunanshi ya,ce ya ji dadin yadda yake ganin sauye sauye a gurin matasa wajen dawowa hanya Mai kyau, yace Kuma su aikin,su shine dama fadakar da jamma, a gaskiya musamman lokacin da wata baraka ke tunkaro su
Ya Kara da cewa zasu cigaba da jajircewa wajen fadakar da wadanda Basu fahimtaba
