Connect with us

News

Ƴan bindiga sun kashe mutum biyu a Katsina

Published

on

Yan bindiga

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa ƴan fashi sun kashe mutum biyu lokacin da suka kai hari a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara.

Sai dai rundunar ta ce jami’anta sun samu nasarar koran ƴanfashin tare da ƙwato mutum 18 waɗanda aka yi yunkurin sacewa.

Advertisement

An ceto mutumin da ya kwashe shekara 20 a kulle a Kaduna

Mai magana da yawun rundunar ƴansanda a jihar ta Katsina, SP Gambo Isa ya ce mutane biyun da suka mutu an hallaka su ne kafin ƴansandan su kai ɗauki.

Advertisement

Maharan a kan babura sun kai farmaki ne a kauyen na Gidan Baushe da tsakiyar daren Laraba.

Sai dai bayan da aka sanar da ƴansanda game da harin, sun kai ɗauki cikin hanzari inda suka kori maharan tare da ƙwato wasu daga cikin mutanen da suka sace

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending