News
An Yi Garkurwa Da Hafsan Dan Sanda A Kwara
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani hafsan dan sanda mai mukamin Mataimakin Sufirtanda, (ASP) Abdulmumini Yusuf, a yankin Ilori, babban birnin Jihar Kwara.
Aminiya gano cewa cewa a ranar Talata da dare ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da ASP Abdulmumini a lokacin da yake kokarin shiga gidansa unguwar Ogidi da ke garin Ilori.
A ranar Alhamis Kwamishinan ’Yan Sandna Jihar Kwara, Paul Odama, ya ce, “Tabbas gaskiya ne, amma muna kan aiki a kan lamarin.”
An ceto mutumin da ya kwashe shekara 20 a kulle a Kaduna
Kakakin rundunar, SP Okasanmi Ajayi, ya ce babu cikakken bayani game da yadda abin ya farku, amma duk da haka, suna aika kai da fata domin ceto hafsan dan sandan da ’yan bindiga suka sace.
Wani mazaunin unguwar Ogidi mai suna Jamiu Abdulganiy ya ce sace dan sandan ya jefa yankin cikin zullumi da mamaki.
Amma kakakin ’yan sandan jihar, SP Ajayi, ya ce, “Duk da girman abin da ya faru, hakan bai sanyaya wa rundunarmu gwiwa ba a aikinmu na kare rayuda da dukiyoyin jama’a.”
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
