Connect with us

News

An ceto mutumin da ya kwashe shekara 20 a kulle a Kaduna

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ƙaddamar da bincike kan dalilan da suka sanya aka kulle wani mutum a cikin ɗaki na tsawon shekara 20.

A ranar Laraba ne ƴansandan suka ceto mutumin mai suna Ibrahim Ado, mai kimanin shekara 67 a wani yanki na birnin Kaduna da ake kira Bayajida.

Rarara ya yiwa ganduje shagube a sabuwar wakar sa

Advertisement

Mai magana da yawun rundunar ƴansanda a jihar Kaduna ASP Muhammed Jalige, ya ce jami’an rundunar sun kai samame a gidan da aka kulle mutumin ne bayan samun bayanan sirri.

Ya ce mutumin mai kimanin shekara 67 ya kwashe tsawon shekarun ne yana garƙame a ɗakin, inda a nan yake cin abinci da kuma duk lamurransa.,, kuma an same shi cikin mummunan yanayi.

Yanzu haka dai mutumin na samun kulawa a asibiti.

BBC NEWS

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending