News
Shugabar ƙasar Tanzania ta nemi mata su rage haihuwa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta bayyana damuwa kan yawan haihuwar da ake yi a ƙasar tare da neman ƴan ƙasa da suk ɗauki matakan rage haihuwa.
Wannan wani gagarumin sauyi ne daga matsayar wanda ta gada, marigayi John Magufuli, wanda ƙarara ya nuna goyon bayan kar mata su yi tsarin iyali.
Faransa za ta horas da sojojin Ukraine 2000
Shugaba Samia ta yi wannan magana ce kan haihuwa gaba gaɗi a ƙasar a ƙarshen makon da ya wuce, a lokacin da ta kai ziyara yankin Geita da ke yammacin ƙasar.
“A jiya a mazaɓarn Buselesele da ke yankin Geita an gaya min ce akwai wata cibiyar lafiya da ake haifar yara 1,000 duk wata.
“To yanzu ajujuwa nawa za a buƙata bayan shekara uku? Cibiyoyin lafiya nawa za a buƙata don duba lafiyar yaran nan?
“Tan ɗin abinci nawa za a buƙata? Ya kamata mu rage yawan haihuwar nan,” in ji shugabar ƙasar.
A shekarar 2018 a yayin da ya halarci wani gangami a yammacin Tanzania, tsohon shugaban ƙsarMagafuli ya bayyana masu tsarin iyali a matsayin ragwanci.
Sannan a 2016, bayan ƙaddamar da ilimin firamare da sakandare kyauta a ƙasar, ya ce: “Mata su yi watsi da duk wani tsarin iyali. Ilimi kyauta ne yanzu.”
-
News24 hours ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
