Connect with us

News

ICPC ta rufe jami’o’i da kwalejojin fasaha 68 na bogi a Najeriya

Published

on

ICPC ta kwashe tana gudanar da wani bincike a boye

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

Advertisement

 

Hukumar da ke yaki da almundahana da sauran lafukan da suka shafi cin hanci ta ICPC a Najeriya, ta ce ta rufe jami’o’i da kwalejin kimiyya da fasaha da ke bayar da shaidar digiri na bogi 62 a fadin kasar.

Advertisement

Hukumar ta ce wannan abu ne da ke neman zama ruwan dare a Najeriya, domin kuwa babu wata jiha a fadin kasar da ba a samu irin wannan makarantu ba a cikinta.

Kotu ta yanke wa dan China hukuncin daurin shekara biyar a jihar Kwara

Advertisement

Cikin shekaru da ICPC ta kwashe tana gudanar da wani bincike a boye, ta kai ga gano adadin makarantu da suka hada da jami’o’i da kwaleji-kwaleji 62 na bogi da ke bayar da shaidar digiri a fadin Najeriya.

Amma ta ce an fi samun irin wadannan makarantu a arewa ta tsakiyar Najeriya.

Advertisement

Hukumar ICPC ta ce ta bayyana wannan gagagrumar barna ne, domin shaida wa ‘yan Najeriya cewa tana kallon duk wani mai shirin yin al-mundahana a kowanne fanni.

Ta ce ko da za a dauke kai a ko ina, to ba dai a bangaren ilimi ba, domin kuwa duk kasar da ba ta da tsarin ilimi ingantacce, to gobenta za ta iya kasancewa cikin kila wa kala.

Advertisement

Muhammad Ashiru Baba shi ne shugaban sashen wayar da kan jama’a na hukumar ICPC, ya kuma ce abin takaici ne halin da ilimi ya tsinci kansa a Najeriya.

Ya kara da cewa ”mafi yawan Jami’o’in ba su da ginin kansu, a maimakon haka suna amfani da gine-ginen Sakandire da na Furamaren da ba a karatu a karshen mako domin gudanar da karatunsu, kuma cikin shekara guda mutum zai samu shaidarsa”.

Advertisement

Wanda hakan ke nufin iyayen da suke kai yaransu irin wadannan wurare, sun kwana da sanin inda suke kai yaran nasu ba wajen kwarai ba ne.

Ashiru Baba ya ce a kwanakin baya har kama sansanin ‘yan bautar kasa suka yi na boge, wani abu da suka jima yana daure musu kai.

Advertisement

ICPC ta cimma nasarar kulle wadannan jami’o’i ne ta hanyar bayanai da ta samu daga hukumar da ke kula da Jami’o’i ta Najeriya NUC, kuma tun daga 2016 take gudanar da wannan aiki har ya zuwa yau.

BBC HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending