News
Murabus ɗin Truss: Boris Johnson ko Rishi Sunak na kan gaba wajen zama Firaministan Birtaniya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Boris Johnson da Rishi Sunak a yau Juma’a su ne ke kan gaba wajen neman maye gurbin Firaminista Liz Truss ta Birtaniya tare da ƴan takarar da ke neman goyon baya don zama shugaban jam’iyyar Conservative a cikin kara wa ta gaggawa.
Bayan da Truss ta yi murabus a jiya Alhamis, wanda ya kawo karshen mulkinta na tsawon makonni shida, masu son maye gurbinta na kokarin samun kuri’u 100 daga ƴan majalisar jam’iyyar Conservative da ke bukatar tsayawa takara a zaben da jam’iyyar ke fatan za ta sake farfado da karfinta.
Sauro na ci gaba da addabar jama’a a Kano
A yayin da jam’iyyar Conservative ke fuskantar zaɓen ƙasa mai zuwa, a cewar ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a, ana sa ran za a gudanar da fafatawa a zaben da zai sanya ta zama ta kafa mulki a Birtaniya sau biyar a shekaru.
Za a sanar da wanda ya yi nasara a ranar Litinin ko Juma’a mako mai zuwa.
A cikin abin da zai zama mi’ara-koma-baya na ban mamaki, Johnson, wanda ƴan majalisar dokoki suka tsige sama da watanni uku da suka gabata, yana kan gaba tare da Sunak don a nada shi Firaminista na gaba.
“Na san yana da wannan ingantaccen tarihin na kawo gyara. Zai kawo gyara. Kuma na tabbata abokan aiki na suna jin wannan saƙon da ƙarfi kuma a sarari,” Dan majalisar masu ra’ayin mazan jiya Paul Bristow ya ce game da Johnson a gidan rediyon LBC.
“Boris Johnson na iya lashe babban zabe na gaba,” in ji shi
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
