Connect with us

News

Shugabar matan jam’iyyar NNPP ta taya Dr Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekaru @66 

Published

on

DAGA   YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

Shugabar matan jam’iyyar New Nigerian People’s Party NNPP ta jahar kano Hajiya Zuwairiya Abubakar ta taya Dr Rabiu Musa Kwankwaso Murnar cika shekara sittin da shida da haihuwa

Tabaiya na hakan ne yayin tattaunawa da wakilin jaridar indaranka a Kano.

Advertisement

 

NNPP ta nemi a binciki ɗan Ganduje, Abba, bisa zargin amfani da motocin gwamnati don yin kamfen

 

Hajiya Zuwairiya ta bayyana Kwankwaso a matsayin gwarzon namiji kuma mai kwazo a tsakanin yan Najeriya. Ta ce Kwankwaso ya zama wata gada wajan samarwa da matasa ilimi da aikin yi a kano da ma kasa biki daya.

Kwankwaso wand a halin yanzu shine dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria People Party ya cancanci a yi murna saboda irin gudunmawar da ya bayar lokacin da yayi Ministan tsaro da kuma gwamnan kano da kuma Sanatan kano ta tsakiya, yasamar da aiyukan cigaban al, umma kamar ilimi, harkar lafiya, samar da aikin yi, samawa mata jari da dai sauransu.

 

Advertisement

Tace Kwankwansoya yi alkawarin sanya ilimi da ci gaban matasa a gaba idan ya ci zaɓe.

 

 

A madadin kaina, da iyalina, al’ummar jahar kano da daukacin magoya bayan jam’iyyar NNPP muna taya murna DR Rabi’u Musa Kwankwaso cika shekaru sittin da shida na hidima ga al, ummar kano dama kasa baki daya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending