News
Buhari Ya Karrama Jonathan da Wike Da Lambobin Yabo Kan Kwarewar Aiki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da kuma tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan lambobin yabo kan kwarewar aiki a wani biki da aka yi a fadar shugaban Kasar da ke Abuja.
Ga baki daya fitattun ‘yan kasar 44 aka karrama da lambar yabon wadda aka kira da Nigeria Excellence Award in Public Service (NEAPS).
Shugabar matan jam’iyyar NNPP ta taya Dr Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekaru @66
Wadanda aka karraman sun hada da gwamnonin jihohin kasar 16 da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da kuma manyan hafsoshin rundunonin soji na kasar nan.
A jawabinsa Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustafa wanda ofishinsa ne ya jagoranci shirya bayar da wannan kyautar da hadin wata cibiya mai zaman kanta da ake kita TBS, ya ce an fito da bayar da kyautar ne domin karrama wadanda suka nuna gogewa wajen yi wa kasar hidima a dukkan matakai.
Gwamna Umaru Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa na daga cikin gwamnonin aka ba kyautar ta NEAPS wadda ita ce irin ta farko a kasar nan.
Wadanda suka shirya bayar da wannan yabon dai sun ce kafin mutum ya cancanci samun wannan lambar yabon dole ne ya kasance jami’in gwamnati ko mutum mai zaman kansa da da ke raye wanda ya nuna bajinta a fannin da yafi kwarewa kuma ya kasance mai halaye na-gari.
