News
Zan sake tsayawa takara – Borin Johnson
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jam’iyyar Conservative mai mulki a Birtaniya na fara hutun ƙarshen mako cikin zazzafar siyasa a yunƙurin da take yi na zaɓen sabon Firaiminista bayan murabus ɗin Liz Truss.
Waɗanda ke zawarcin kujerar na da zuwa Litinin su samu goyon bayan ƴan majalisa.
Ƙwallon mata: Najeriya ta kai wasan kusa da ƙarshe a Kofin Duniya
Ana buƙatar wanda zai nemi tsayawa takarara firaiminista ya sami aƙalla yan majalisa 100 na goyon bayansa.
Tuni dai Rishi Sunak ya ce ya kusan kai wannan adadi.
Sai dai hankalin jama’a ya karkata kan tsohon firaiminsta Boris Johnson wanda zai koma Landan daga yankin Caribbean inda ya tafi hutu.
Rahotanni sun ce Mista Johnson ɗin ya ƙenƙyasa wa wani makusancinsa cewa a shirye yake ya fito takara.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
