News
Shugaban Jamus da na Faransa za su gana kan tsamin dangantakar kasashen .
Nan gaba kadan ne shugabannin kasashen Jamus da Faransa za su fara ganawa a birnin Paris, a daidai lokacin da dangantaka tsakanin kasashen biyu ke nuna alamun yin tsami.
An dage taron hadin gwiwa tsakanin ‘yan majalisun kasashen biyu wanda a baya aka shirya gudanarwa yau.
Ya Kamata A Ayyana Dokar Ta-Baci A Fannin Lafiyar Najeriya —Likitoci
A taron kungiyar Tarayyar Turai a makon da ya wuce, shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana cewa Jamus na tsaka mai wuya a kokarin da ta ke yi na kebe kan ta.
Wannan batu ya janyo guna-guni, da ake dangantakawa da batun farashin iskar gas, da batun dala biliyan 200 da Jamus ta zuba a fannin makamashi domin tallafa wa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da iyalai.
BBC HAUSA
Advertisements
