News
Jiragen yaƙin Turkiyya marasa matuƙi na gab da isowa Najeriya’
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jakadan Turkiyya a Najeriya Hidayet Bayraktar ya ce jiragen helikwafta da marasa matuƙi da ƙasarsa ke ƙerawa za su isa Najeriyar nan ba da jimawa ba da zimmar tallafa wa ƙasar wajen yaƙi da matsalar tsaro.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ambato Bayraktar na magana yayin bikin Ranar Tarayyar Turkiyya karo na 99 da aka gudanar a ofishin jakadancin ƙasar da ke Abuja ranar Asabar.
Gangar ɗanyen mai dubu 700 a ke sace wa kullum a Nijeriya – Minista
Ya bayyana yunƙurin a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar da ƙasashen suka ƙulla a 2021, yana mai cewa Turkiyya za ta faɗaɗa taimakon da take bai wa Najeriya wajen yaƙi da barazanar tsaro.
“Yarjejeniyar da ƙasashenmu suka saka wa hannu a shekarar da ta gabata abu ne na tarihi,” a cewarsa.
“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa nau’i biyu daga cikin jiragen yaƙinmu irinsu na farko, maras matuƙi na Bayraktar (TB-2) da helikwafta (T-149) ATAK na gab da isowa Najeriya.
“Muna da ƙwarin gwiwa cewa sabbin kayan yaƙi na Turkiyya za su taimaka wa gwamnatin Najeriya wajen samar da zaman lafiya da kare dukiyar ‘yan ƙasa.”
-
News7 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News6 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News7 days ago
Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

