News
Kudin da aka ware don yaki da labaran ƙarya sun yi kadan – Lai Mohammed
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Mnistan ƴada labaru da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce kudaden da ake ware wa ma’aikatarsa sun yi kadan wanda kuma ke kawo cikas wajen ƴaki da labaran ƙarya da kuma kalaman batanci.
Ministan ya bayyana hakan ne yau Talata a gaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa a 2023.
Kotu a Bauchi ta yanke wa wani saurayi da ya kashe abokinsa hukuncin kisa
Ya ce ma’aikatarsa na bukatar kudade da ya kamata domin ƴaki da labaran ƙarya da kuma kalaman batanci.
“Idan akwai ma’aikatar da ya kamata a ware wa kudade da yawa, to ita ce ma’aikatar ƴada labaru,” in ji Lai.
Ya ce duk da cewa an yi watsi da gargadin da Amurka ta bai wa ‘yan kasarta a Najeriya kan batun rashin tsaro a Abuja, amma ba a yi hakan ba yadda ya kamata na ganin hankalin ‘yan Najeriya ya kwanta.
Ya kuma ce abin damuwa shi ne duk da cewa a ware wa ma’aikatar naira biliyan 2.5 a matsayin kudaden kashewa a 2022, kashi daya bisa uku na kudin shi aka sak ware mata na shekarar 2023 wanda kuma ya kai naira miliyan 869.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
