Connect with us

Sports

An hada Liverpool da Real Madrid a Champions League

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Liverpool da Real Madrid za su kara a wasan zagaye na biyu a Champions League, bayan da aka raba jadawali ranar Litinin a Nyon, Switzerland.

 

Advertisement

A bara a Faransa Real Madrid ta doke Liverpool ta lashe kofin, kuma na 14 jumulla.

 

Advertisement

Kungiyoyin biyu sun kara sau tara a tsakaninsu a gasar Zakarun Turai, inda Real ta ci biyar, Liverpool ta yi nasara a uku da canjaras daya.

 

Advertisement

Real Madrid ce ta ja ragamar rukuni na shida da maki 13, Liverpool kuwa ita ce ta yi ta biyu a rukunin farko da maki 15 iri daya da na Liverpool.

 

Advertisement

Real Madrid ce za ta fara kai ziyara Anfield a wasan farko na zagaye na biyu ranar 14 ko 15 ko 21 ko 22 ga watan Fabrairu.

 

Advertisement

Za kuma ta karbi bakuncin Liverpool a zagaye na biyu a Santiago Bernabéu ranar 7 ko 8 ko 14 ko 15 ga watan Maris.

 

Advertisement

Real Madrid tana da Champions League 14, ita kuwa Liverpool tana da guda shida, kenan a tasakaninsu an dauki kofin sau 20 kenan.

 

Advertisement

Jadawalin wasannin zagaye na biyu:

 

Advertisement

RB Leipzig v Manchester City

Club Bruges v Benfica

Advertisement

Liverpool v Real Madrid

AC Milan v Tottenham

Advertisement

Eintracht Frankfurt v Napoli

Borussia Dortmund v Chelsea

Advertisement

Inter Milan v Porto

PSG v Bayern Munich

Advertisement

Tun farko an raba kungiyoyi 16 zuwa tukunya biyu, ta farko wadda ta kunshi wadanda suka ja ragamar rukuninsu, sai tukunya ta biyu ta wadanda suka yi na bibiyu a rukunin.

 

Advertisement

Wadanda suka yi na bibiyu a rukuninsu sun hada da Liverpool da Brugge da Inter da Eintracht Frankfurt da Milan da Leipzig da Dortmund da kuma PSG.

 

Advertisement

Jerin wadanda suka yi na daya a kowanne rukuni: Bayern, Benfica, Chelsea, Manchester City, Napoli, Porto, Real Madrid da kuma Tottenham.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending