News
Sarkin Saudiyya ya ba da umarnin yin sallar roƙon ruwa a masallatan ƙasar
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Sarkin Saudiyya Salman Bn Abdul’aziz ya bai wa masallatan ƙasar umarnin gabatar da sallar roƙon ruwa a ranar Alhamis mai zuwa.
Titunan Nijeriya duk sun mutu, in ji FERMA
Shafin Facebook da ke kula da Masallatai
Biyu Masu Daraja na Makkah da Madina na ne ya sanar da hakan a yau Litinin.
Sarki Salman ya ce cikin masallatan da za a yi sallar roƙon ruwan har da na Ka’aba da na Manzon Allah da ke Madina.
Advertisements
