Connect with us

News

Kotu ta soke zaɓen fidda gwanin gwamna na jam’iyyar APC a jihar Akwa Ibom

Published

on

APC

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Uyo babban birnin Akwa Ibom ta soke zaɓen fidda gwani na takarar gwamna a jam’iyyar APC wanda ya bai wa Akan Udofia nasara.

Advertisement

Kotun ta yanke hukuncin cewa Akan Udofia ba halastaccen ɗan jam’iyyar APC ba ne.

Yayin da take yanke hukuncin mai shari’a Agatha Okeke ta bayar da umarni ga jam’iyyar da ta sake gudanar da wani zaɓen fidda gwanin a jihar cikin mako biyu masu zuwa.

Advertisement

Tsohon mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin Niger Delta Ita Enang ne ya shigar da ƙara a gaban kotun yana ƙalubalantar takarar mista Udofia.

Mista Enang ya yi zargin cewar Udofia ba ɗan jam’iyyar APC ba ne a lokacin da aka gudanar da zaɓen fidda gwanin, kasancewa ya shiga takarar fidda gwani da jam’iyyar PDP ta gudanar ranar 25 ga watan Mayu, kafin daga bisani ya shiga takara a zaɓen fidda gwanin da jam’iyyar APC ta gudanar ranar 26 ga watan na Mayu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending