Connect with us

News

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin sanya wa shanu ɗan-kunne

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin maƙala wa dabbobi ɗan-kunnne mai amfani da fasahar zamani

Advertisement

Ɗan-kunnen zai taimaka ne wajen sanin tarihi da bayanan da suka shafi dabba da kuma bin labinta a duk inda take.

‘Akwai Masu Fada Aji Da Ke Neman Halasta Tabar Wiwi A Najeriya’

Advertisement

Gwamnatin ta ƙaddamar da shirin ne tare da haɗin-gwiwa da ƙungiyoyin makiyaya da nufin magance matsalar satar shanu da inganta kasuwancinsu a gida da wajen Najeriya.

Gwamnatin Najeriyar ta bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata a cusa fasahar zamani a cikin harkar kiwo ta yadda za ta ci gajiyar cigaban a da ake samu.

Advertisement

Shirin, a cewar gwamnati zai taimaka wajen magance matsalolin da makiyaya ke fama da su kasar, musamman satar shanu, da rashin rumbun bayani a kan dabbobi da zai taimaka wajen fito da tsare-tsare na inganta harkar kiwo fataucin dabbobi ko nama da sauran abubuwan da suke samarwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending