Connect with us

News

Sojan Najeriya Ya Bude Wa Abokan Aikinsa Wuta A Borno

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Wani soja ya bude wuta a wani sansanin sojoji da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya inda ya kashe soja guda da wani ma’aikacin agaji tare da raunata wani matukin jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar Dinkin Duniya.

 

Advertisement

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa tana mai cewa sojojinta da ke wurin sun yi nasarar kashe sojan da ya kai harin a jihar ta Borno.

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin sanya wa shanu ɗan-kunne

Ta kuma bayyana shi a matsayin ‘bijirarren soja’.

Advertisement

 

Rundunar sojin Najeriyar ta kuma ce : An wuce da matukin jirgin da aka raunata zuwa asibiti kuma yana samun kulawar da ta kamata

Advertisement

 

Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin da ya sa sojan ya kai wannan harin ba.

Advertisement

 

Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis da rana.

Advertisement

 

Rundunar sojin Najeriyar ta ce an fara gudanar da cikakken bincike a kan ”abin takaicin da ya faru.”

Advertisement

 

Dubban sojojin Najeriya na ci gaba da gwabza fada da kungiyar Boko Haram da kuma reshenta da ake kira ISWAP a arewa maso gabashin kasar a cikin shekaru sama da 10.

Advertisement

 

Kungiyoyin agaji na cikin gida da na kasa da kasa na tallafa wa miliyoyin mutane da rikicin ya daidaita wanda kuma ya yi sanadin mutuwar mutum kusan dubu 350 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending