Business
Dala Ce Ta Haddasa Tsadar Man Fetur – IPMAN
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya IPMAN ta dora alhakin karancin man a Lagos da Abuja da sauran jihohin kasar kan tsadar farashin Dala da kuma yadda Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya gaza sakin wadataccen man.
Akwai dogayen layukan ababen hawa a sassan Lagos da Abuja duk da cewa, ana sayar da lita guda akan farashin Naira 180 ko ma fiye da haka.
Matsalaar ta karancin man ta tilasta wa direbobin motocin haya tsauwala kudin mota ga fasinjoji.
Jami’in Hulda da Jama’a na Kungiyar IPMAN, Chief Ukadike Chinedu ya ce, manyan jiragen ruwa na shigo da man fetur cikin Najeriya ta kan iyakar Lagos, yayin da kananan jiragen ruwa ke kai man zuwa tashoshin jiragen ruwa na Lagos da Warri da Fatakwal da dai sauransu.
Dole ne Matasan Najeriya su yi adawa da masu kawo cikas ga makomarsu – Obasanjo
Sai dai a cewarsa, hatta kananan jiragen ruwan, ana biyan su ne da Dalar Amurka.
Jami’in ya bayyana cewa, mawuyaci ne masu gidajen man su sayar da shi akan Naira 145 kowacce lita a daidai lokacin da farashin hayan jirgin ruwan ya karu daga Dala dubu 38 zuwa Dala dubu 108.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
