Connect with us

News

An mika bayanin harajin da Trump ke biya ga majalisa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Baitul-malin Amurka ya mika wa wani kwamitin majalisar dokokin kasar takardun da ke kunshe da bayanan harajin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ke biya.

 

Advertisement

Hakan ya biyo bayan hukuncin da Kotun Kolin kasar ta yanke ne a makon da ya gabata, inda ta bayar da umarnin bai wa kwamitin da ‘yan jam’iyyar Democrat ke jagoranta takardun, na tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2020.

Rikicin Siyasa Ya Ci Rayuka 1,525 A Najeriya —Rahoto

Wani kakakin Baitun-malin ya ce hukumar ta bi umurnin kotun amma kuma ya ki ya ce uffan game da cewar ko takardun sun kai ga hannun ‘yan kwamitin zuwa yanzu.

Advertisement

 

BBC ta rawaito cewa Mista Trump ne shugaban Amurka na farko a cikin shekara arba’in da ya yi kememe ya ki bayar da takardun harajinsa.

Advertisement

 

Ya kafe cewa kwamitin na neman yi masa bita-dakullin siyasa ne kawai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending