News
An bai wa Majalisar Kano shawarar hukunci mai tsanani wajen kafa dokar haƙƙin yara
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A ranar Alhamis Majalisar Dokokin Jihar Kano a arewacin Najeriya ta yi zama don sauraron ra’ayoyin jama’a a kan yunkurin kafa dokar kiyaye haƙƙin ƙananan yara.
Mahukunta da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kiyaye hakkokin yara sun ba da shawarar a yi tanadin hukunci mai tsanani ga masu tauye haƙƙin yaran, ciki har da ɗaurin shekara bakwai da tara mai yawa ga masu cin zarafin su.
Majalisar Kanon ta bayyana cewa suna yunkurin kafa dokar ne saboda a hukunta masu kuntata musu, kuma wannan ne ya sa aka yi tanadin hukunce-hukunce daban-daban.
Mataimakin Kakakin Majalisa Kabiru Hassan Dashi – kuma shugaban kwamitin harkokin mata da walwalar jama’a – ya faɗa wa BBC Hausa cewa dokar za ta ba da dama agina wa marayu gidaje da ɗaukar nauyin karatunsu.
Ya ƙara da cewa wannan ne zama na ƙarshe da suka yi kafin amincewa da dokar a Majalisa.
