News
Yan bindiga sun sace iyalan ɗan majalisa a Jihar Zamfara
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
‘Yan bindiga sun sace iyalan wani ɗan Majalisar Ddokokin Jihar Zamfara a garin Jangebe da ke jihar.
‘Yan bindgar da ake zaton masu garkuwa da mutane ne domin karɓar kuɗin fansa sun dirar wa gidan Honorabul Aminu Yusuf Ardo ne jiya Alhamis da dare, inda suka sace matarsa da duka ya’yansu hudu ƙanana.
INEC za ta sauya wa rumfunan zaɓe 357 waje a Katsina sabo da rashin tsaro
Sun kuma sace wasu maƙwabtan dan siyasar, kamar yadda wani mazaunin unguwar da gidan ɗan majalisar yake ya shaida wa BBC.
Advertisements
