Entertainment
Wandon Mawaki Asake Ya Barke Yana Tsaka Da Rawa A Kan Dandamali
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Fitaccen mawakin Najeriya, Ahmad Ololade, wanda aka fi sani da Asake, ya yage yana tsaka da waka kan dandali a London.
Lamarin ya auku ne yayin da mawakin yake rera wakar ‘Loaded’ da suka yi tare da fitacciyar mawakiyar Najeriya Tiwa Savage, inda ya cilla kafarsa a wani salon rawa, kuma hakan ya sa wandonsa take ya yage har farin dan kamfansa ya bayyana.
Asusun lamuni na duniya zai bai wa Ghana taimakon dala biliyan uku
Daga nan ne cikin jin kunya ya ci gaba da rawa yana ja baya, har ya bar dandalin.
Tuni dai bidiyon ya gama karade kafafen sada zumunta, inda wasu suka fara sanya bidiyon kwaikwayonsa, ta hanyar yaga wandunansu, da sanya farin dan kamfai a ciki.
