Connect with us

Entertainment

Badakala: ICPC Ta Saki D’banj Bayan Sa’o’i 72 A Tsare

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

An saki fitaccen mawakin nan, Daniel Oladapo, wanda aka fi sani da D’Banj, bayan tsare shi gwamnati ta yi kan zargin badakalar kudaden shirin N-Power.

Advertisement

 

An sake shi bayan shafe sa’o’i 72 a hannun Hukumar Yaki da Ayyukan Zamba (ICPC), bisa zarge-zargen damfara da ke da alaka da shirin N-Power.

Advertisement

Buhari Ya Amince Da Siyo Jiragen Yaki

 

Shirin N-Power dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya kirkiro shi a ranar 8 ga watan Yuni, 2016, domin magance matsalolin rashin aikin yi da karfafawa matasa gwiwa.

Advertisement

 

Aminiya ta ruwaito yadda fitaccen mawakin ya shiga hannun ICPC, bayan kin amsa goron gayyata da hukumar ta aike masa.

Advertisement

 

 

Advertisement

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, lauyan D’banj, Pelumi Olajengbesi, ya ce an saki mawakin bayan hadin kai da ya bai wa hukumar a binciken da take gudanarwa kan lamarin.

 

Advertisement

Sai dai bai bayyana ko hukumar ta bayar da belin mawakin ba.

 

Advertisement

Sanarwar ta kara da cewa, “Bayan shafe sa’o’i 72 a tsare ba bisa ka’ida ba da kuma zargin badakala da ake wa Mista Daniel Oladapo (D’banj), hukumar ICPC ta saki fitaccen mawakin da yammacin ranar Juma’a.

 

Advertisement

“ICPC ta saki D’banj ne bayan ta kasa gano wani laifi a tattare da shi.

 

Advertisement

 

“Dole ne mu bayyana wa ’yan Najeriya gaskiyar lamari cewar D’banj kan aikata laifin da ake zargin sa da shi.

Advertisement

 

“Abin kunya ne a daganta badakalar Naira miliyan 900 da irin wannan fitaccen mutum ba tare da wata shaida ba.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending