News
MDD ta yi kira da a kai dauki ga fasinjojin jirgin ruwan da suka makale a tekun Andaman su 150
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashen da ke kusa da tekun Andaman ta su kai dauki ga wani jirgin ruwa da ya dauko mutane akalla ‘yan gudun hijirar Rohingya 150 daga Myanmar.
Jirgin ya kasance babu wutar lantarki a cikinsa tsawon makonni uku.
Mutanen da ke cikin jirgin da aka samu ji ta bakinsu ta wayar tauraron dan adam, sun ce basu da ruwa da abinci.
Fasinjojin cikin jirgin sun hadar da mata da yara, kuma akwai rahotannin da ke cewa akwai wadanda suka mutu a cikinsu.
Rahotanni sun ce ‘yan gudun hijirar Rohingya sun bar sansanonin da suke zaune a kudancin Bangladesh sun nufi Malaysia.
Advertisements
