News
Buhari zai sanya hannu kan kasafin kudin 2023 ranar Talata – Ahmed Lawan
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban majalisar dattijai Ahmed Lawan, yace shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai sanya hannu kan kasafin kudin 2023 a ranar Talata 3 ga watan Janairun 2023.
Jaridar Dailyt Trust ta rawaito cewa Lawan ya bayyana hakan ne bayan tattaunawar da suka yi ta musamman da shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja.
Shugaban Majalisar ya isa zauren majalisar ne da misalin karfe 3 na yamma, ya kuma ce sun tattauna bukatar karin karbar aron kudi da kuma maganar kasafin kudin 2023.
Advertisements
