News
Kwamishiniya Ta Yi Murabus Bayan An Tube Wa Mahaifinta Rawani
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Kwamishinar Bunkasa Kungiyoyi, Kananan da Matsakaitan Sana’o’i ta Jihar Bauchi, Sa’adatu Bello Kirifi, ta ajiye mukaminta, bayan an sauke mahaifinta daga sarauta.
Aminiya ta rawaito cewa tube wa mahaifinta rawaminsa na Wazirin Bauchi.
Sa’adatu Bello Kirifi ta yi murabus ne kasa da awa 24 bayan an ube wa mahaifin nata, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, rawaminsa na Wazirin Bauchi tare da sallamar sa daga Majalisar Masarauar a ranar Talata .
A takardar ajiye mukamin da ta aike wa Gwamna Bala Mohammed ranar Laraba, Honorabul Sa’adatu ta ce, “Mai Girma Gwamna, ina mika takardata ta yin murabus daga Majalisar Zartarwa da kuma kujerar Kwamishinar Bunkasa Kungiyoyi, Kanana da Matsakaitan Sana’o’i ta Jihar Bauchi, ba tare da bata lokaci ba.
“Ina godiya ga Gwamna da ya ba ni damar yi wa Jihar Bauchi aiki a gwamnatinka.”
