Connect with us

News

Sama da mutum miliyan shida ba su karɓi katin zaɓensu ba – INEC

Published

on

Katin zaɓe

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

Advertisement

 

A yayin da ya rage ƙasa da mako takwas a gudanar da babban zaɓe a Najeriya , Hukumar zaɓen ƙasar ta ce akwai aƙalla mutum miliyan 6.7 da ba su karɓi katunan zaɓensu ba.

Advertisement

 

Wani rahoto da ya fito daga ofisoshin INEC a jihohin ƙasar ranar Talata ya nuna cewa akwai katuna kusan miliyan 6.7 da ke ƙunshe cikin ofisohin INEC a jihohin ƙasar 17 da kuma babban birnin tarayyar ƙasar Abuja.

Advertisement

’Yan Bindiga Sun Sake Kone Ofishin ’Yan Sanda A Imo

Tun da farko dai Hukumar Zaɓen mai Zaman ƙanta a Najeriya ta bayyana cewa za ta fara rabar da katunan zaɓen daga watan Disamban da ya gabata zuwa ranar 22 ga watan Janairun da muke ciki.

 

Advertisement

Babban kwamishinan hukumar kuma shugaban kwamitin yada labarai da ilimantar da masu kaɗa ƙuri’a, Festu Okoye ya faɗa a wata sanarwa da ya fitar cewa daga ranar 6 zuwa 15 ga watan Janairu za a mayar da katunan zuwa mazaɓu domin sauƙaƙa wa jama’a karɓar katin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending