News
DA ƊUMI ƊUMIN SA: CBN ya kara wa’adin kwanaki 10, ƴan Najeriya su canja tsaffin takardun kuɗin da ke hannun su.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babban bankin Najeriya ya kara wa’adin canza amfani da tsohon kudaden Naira. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban bankin ya fitar ranar Lahadi.
A cikin sanarwar, Godwin Emefiele, gwamnan bankin, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari’ ya bayar da izinin kara wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu.
Ya ce ya zuwa yanzu, CBN ya tara tiriliyan 1.9 sannan ya bar biliyan 900 don cimma nasarar aiwatar da manufofin tsarin.
Advertisements
