News
NDLEA ta kama hodar ibilis da ake shirin shiga Turai da ita
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Jami’an Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi na Najeriya sun kama hodar ibilis da wasu muggan ƙwayoyi masu yawa da aka yi niyya shigar da su Turai a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke birnin Legas.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi ta ce ta ƙwace kilogiram 75.75kgs na tabar wiwi da aka shigar da ita ƙasar a ɓoye cikin kwantaina daga Canada.
Mutum uku sun mutu bayan faduwar gini
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an hukumar sun kama wata mace mai ciki, da wani malamin makaranta, tare da ƙwace tan biyu na muggan ƙwayoyin a jihohin takwas da ke ƙasar.
Advertisements
