News
Yan Sanda Sun Kama Wadanda Suyi Garkuwa Da da amarya a Adamawa
Wasu magidanta su biyu, Suleman Adamu da abokinsa Amadu, sun shiga komar ƴansanda a Jihar Adamawa bisa zargin su da yin garkuwa da amarya a ranar da aka kai ta daki.
Rahma Radio FM ta rawaito cewa mutanen sun shiga gidan ne lokacin da angon amaryar, Abubakar ya fita ya sayi kazar siyan baki.
El-Rufa’i ya samar da harkar sufuri da lafiya kyauta da ga ƴan Kaduna
Da ya ke zantawa da manema labarai, angon ya ce mutane biyun, ɗaya makwabcin sa ne, dayan kuma ma surukinsa ne.
A cewar sa, ya fita ne ya sayo wa amarya kaza, shi ne sai su ka afka gidan na sa, inda su ka kwantar da kishiyar amaryar su ka kuma mare ta, tare da razana ta da adda, sai kuma su ka sungume amaryar zuwa cikin jeji.
“Sannan bayan sun kai ta jeji sai su ka kwantar da ita su ka mammare ta,” in ji shi
Da ake tuhumar waɗanda su ka aikata laifin, Suleman Adamu ya ce shi ne ya kitsa tuggun ɗauke amaryar, inda ya ce ji ya yi sha’awar ta ne shi ya sa shi aikata hakan.
Adamu ya ce bayan sun kitsa makircin, sai suka kwankwasa kofar gidan da amaryar ta ke bayan fahimtar cewa mijin nata ya fita, inda su ka sungumo amaryar su ka yi jeji da ita.
Ya ƙara da cewa basu jima da zuwa jejin ba sai ƴansanda su ka gan su, su ka kuma cafke su.
SP Suleman Yahayan Guroje, Kakakin rundunar ƴansanda ta jihar Adamawa ya ce za a gurfanar da magidantan biyu a gaban kuliya manta-sabo.
