News
El-Rufa’i ya samar da harkar sufuri da lafiya kyauta da ga ƴan Kaduna
A jiya Talata ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da samar da motoci da kuma ayyukan kiwon lafiya kyauta na tsawon mako guda domin sauƙaƙa wahalhalun da al’ummar jihar ke fuskanta sakamakon matsalar kudi da ake fama da ita a halin yanzu.
Wata sanarwa da Muyiwa Adekeye, mashawarci na musamman ga gwamna Nasir El-Rufai kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa ya fitar, ta ce an dauki matakin ne a karshen taron majalisar tsaron jihar a Kaduna.
Sai dai ya ce ayyukan sufurin na kyauta za su kasance ne kawai ta hanyoyin da aka kebe a Kaduna, Kafanchan da Zariya.
“Za a yi hakan ne tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin sufuri, waɗanda za su ba da motocin bas da kekuna masu uku.”
Adekeye ya kuma ce duk cibiyoyin kiwon lafiya mallakar gwamnatin jihar za su ba da kulawa ta yau da kullun kyauta ga cututtuka gama gari kamar zazzabin cizon sauro da typhoid.
“Zai kasance baya ga kulawa kyauta ga mata masu juna biyu da yara ‘yan kasa da shekaru biyar wanda tsarin gwamnati ne tun shekarar 2015.
Daily Nigerian
