Politics
Kungiyar ‘yan jaridu na yanar gizo sun taya zaba ben gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf murnar lashe zabe
Kungiyar ‘yan jaridun na yanar gizo sun ta taya zababben gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida murnar lashe zaɓen gwamnan Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jahar kano Yakubu Salisu wada ya rabawa manema labarai
Yace Nasarar Abba ba ta basumamaki ba saboda dimbin farin jini, iya aiki da tarihinsa na tsawon shekaru wanda hakan ya ba shi matsayi na musamman a zukatan al’ummar jihar kano.
Sanarwar ta kara dacewa kanawa sun kyautata zaton cewa zai mayar da jihar Kano cikin bunkasar tattalin arziki, wadata masana’antu da kasuwanci gami da samar da ababen more rayuwa da ci gaban bil’adama.
A matsayinmu na kwararriyar kungiya wacce ta taka rawar gani wajen yada manufofin jam’iyyar NNPP da na zababben gwamnan Kano ga al’ummar Kano, muna alfahari da kasancewa tare da mai girma Abba Kabir Yusuf, kuma mun yi imanin zai samar da ribar dimokuradiyya ga mutanen kirki na jihar.
Tuni dai zababben gwamnan ya nuna shirinsa na gudanar da ayyukan gwaji a jihar cikin gaggarumin salo da ci gaba wanda muke ganin zai kawo cigaban da ake bukata a jihar.
Muna kira ga masu ruwa da tsaki da su hada kai tare da ba shi duk wani goyon bayan da ake bukata domin ciyar da jihar gaba.
