News
Mutum Uku Sun Rasu A yayin da motar ta kone ƙurmus a titin zuwa gidan Gwamnatin A Kano
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta sanar da rasuwar mutum uku sakamakon wani hatsarin mota da ya auku da safiyar Talata a birnin Kano.
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya shaida manema labarai cewa hatsarin ya auku ne a kan gadar sama da ke kan hanyar zuwa gidan Gwamnatin jihar.
Ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar leta-hayis wacce ta taso daga garin Ajingi ta shiga cikin garin Kano, inda a nan ne murfinta ya daki wani bangaren gadar saman.
Hakan a cewar Kakakin hukumar, ya sa motar ta kama da wuta bayan murfin ya fice daga jikinta..
A cewar Saminu, bayan aukuwar hatsarin, jami’ansu sun je wurin inda suka kwashe gawarwaki tare mutanen da suka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda aka tabbatar da rasuwar mutum uku.
Ya ce yanzu haka ragowar wadanda suka jikkata suna can a asibitin suna samun kulawar gaggawa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
