News
Yan bijilante za su kama saurayi da budurwa da ke zance a lokacin sallar Tahajjud
Ƙungiyar Sintirin Bijilante dake Kano ɓangaren kwamandanta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta ce, ta ɗauki gaɓarar zuba jami’an ta a lungu da saƙo na Kano, domin tabbatar da tsaro a lokacin da za’a fara fita sallar dare ta Tuhajjud a yau Litinin, domin kawar da ɓatagari.
Jami’in hulda da jama’a na ƙungiyar kuma Kwamandanta na shiyyar ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a daren Litinin.
Ya ce, ba za su saurarawa duk wasu ɓatagari dake fakewa da sallar dare suna aikata Laifuka ba.
A cewar sa, duk saurayi da budurwar da suka samesu a kan hanya ko lungu da sunan suna yin zance ko kuma yin abinda bai dace ba, zasu ɗauki matakin doka a kansu.
Ya kara da cewa kungiyar za ta zuba jami’anta a duk masallacin da ake sallar dare a Kano, domin tsare dukiyoyi da rayukan jama’a har ƙarshen sallar daren ta Tuhajjudin ba tare da gajiyawa ba.
