Connect with us

News

Wasu  Yan Bindiga Sun Sace Basarake Da Wasu Mutum 13 A Abuja

Published

on

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake tare da wasu mutum 13 a Yankin Babban Birnin Tarayya.

A cikin dare ne ’yan bindigar suka kutsa cikin kauyen Chida da ke Karamar Hukumar Kwali suka yi awon gaba da mutanen.

Advertisement

Goman Karshe: Dama Ta Karshe Ga Mai Neman Rahamar Allah

Gudun Kayayyakin Da Aka Yi A Kasar
Wani dan unguwar mai suna Ishaya Musa, ya bayyana cewa maharan sun kuma harbi wani matashi mai shekara 18 da ya yi kokarin tserewa.

Ishaya Musa ya bayyana cewa a daren Juma’a maharan suka shigo suna harbi da bindigogi kirar AK-47 suka je kai-tsaye zuwa fadar basaraken suka dauke shi, kafin daga bisani su dauke sauran mutanen.

Advertisement

A cewar Ishaya, “Saboda firgita da karar harbe-harben, yaron ya yi kokarin tserewa, shi ne suka harbe shi a kafa, amma an kai shi asibiti.”

Aminiya ta rawaito cewa Sauran mutanen da aka dauke, suna kwakkwance ne a waje ne saboda tsananin zafi, lokacin da aka kai harin.

Advertisement

Ya ce a ranar Asabar da yamma jagoran ’yan bindigar ya kira iyalan wadanda aka sacen ya yi magana da su.

Kauyen Chida na da nisan kilomita uku daga Bukpe, kauyen da a bara ’yan bindiga suka sace basarakensa, Alhaji Hussaini Shamdozhi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending