News
A bar majalisa ta fitar da shugabanci ba ƙarfa-ƙarfa ba – Kawu Sumaila.
Ƙasa da wata biyu a buɗe Majalisar Tarayya ta 10, ana ci gaba da kiraye-kiraye a Najeriya game da tsarin da ya kamata a bi wajen fitar da shugabanninta.
‘Yan majalisa da dama ne tsakanin majalisar dattijai da ta wakila suka ayyana burinsu na samun damar zama mutum na uku da na huɗu mafi girman muƙami a ƙasar.
Illa biyar da rikicin Sudan zai iya haifarwa a kasar zuwa janzo
Sai dai, jam’iyyar APC mai mulki wadda ke da rinjaye a zaurukan majalisar tarayyar ta ce sun yi azarɓaɓi. A cewarta, kamata ya yi su bai wa jam’iyyar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar damar raba muƙaman zuwa shiyyoyin Najeriya.
Amma ana ƙara samun masu kiraye-kirayen cewa a bar dimokraɗiyya ta yi aikinta wajen fitar da shugabancin majalisa ta 10, maimakon fifita muradin wata jam’iyya.
Cikin masu wannan kira, har da zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattijai na jam’iyyar adawa ta NNPP, Onarabul Abdurrahman Kawu Sumaila.
A cewar ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Kano ta Kudu ‘yan majalisar dokoki, al’ummar ƙasa suke wakilta, ba shugaban ƙasa ko jam’iyyarsa ba.
Don haka ya ce kamata ya yi a bar musu wuƙa da nama, su zaɓi shugaban da suke so.
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News7 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
