News
Shin kun taɓa fuskantar dannau yayin bacci?
Daga Farouk Ibrahim Ali
Dannau abu ne da mutane da dama ke fuskanta wanda ke danne mutum yayin bacci, kuma ya hana su tashi.
Ana yawan alakanta dannau da aljanu, amma masana sun sanar da cewa wannan ba haka ba ne.
RANAR MA’AIKATA TA SHEKARAR 2023: Kaso mai yawa na ma’aikatan Najeriya na buƙatar ɗauki.
Sun bayyana cewa dalilin da ya sa ake fuskantar dannau shi ne, idan mutum yana mafarki, akwai ɓangaren ƙwaƙwalwarsa da ke farkawa daga bacci amma kuma sauran ɓangarorin ƙwaƙwalwar ba su farka ba.
Hakan ke sa mutum ya ji kamar ya farka amma kuma gangar jikinsa ba ta farka ba.
Advertisements
