News
RANAR MA’AIKATA TA SHEKARAR 2023: Kaso mai yawa na ma’aikatan Najeriya na buƙatar ɗauki.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A shekarun baya kafin zuwan gwamnatin Buhari, ma’aikata a Najeriya abin sha’awa ne a wajan mutanan gari, saboda yadda suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum a cikin tsari da albashin da suke karɓa.
Kamar yadda yake sanannan abu, ma’aikata da yawa idan aka yi albashi zuwa suke suna siyan kayan abincin da a ƙalla za su yi wata guda suna amfani da shi a gidajen su.
Daya Daga Cikin Motocin Da Ke Kwaso ‘Yan Najeriya a Sudan Ta Kama Da Wuta
Kafin zuwan gwamnatin nan, Buhun shinkafa da Jarkar man girki mai lita 25 ba su kai N7,000 kowanne ba. Kwalin Taliya da na Makaroni babu wanda ya kai N2,000. Amman yanzu Buhun shinkafa da Jarkar man girki mai lita 25 kowannensu ya doshi N40,000. Kwalin Taliya da Makaroni kowanne ya doshi N9,000. Kusan za’a iya cewa, babu abinda bai ninka kuɗinsa sau 4 ko 5 ba.
Daga farkon gwamnatin Buhari zuwa yanzu, bana jin akwai maaikacin da ya sami ƙarin albashi da kaso 100 cikin 100, ga shi kuɗaɗen da ake siyan kayayyakin masarufi sun ninka da sama da kaso 300 wasu ma 400.
Wannan dalilin ya sa mafi yawan ma’aikata, musamman ƙananun maaikata waɗanda su suka fi yawa, ba sa iya riƙe gidajen su kamar yadda suka saba. Wasu daga cikin ma’aikata ma albashin su ko sati baya iya yi musu.
Muna kyautata zaton kafin sabuwar gwamnatin Tinubu ta shafe shekara guda akan mulki, in sha Allahu za’a sami sauƙin wannan tsadar rayuwar da aka jefa ma’aikata da ma al’ummar gari baki ɗaya, amman kafin nan, kamata ya yi gwamnati ta duba yiwuwar ragewa ma’aikata ranakun aiki, ko kuma awannin da suke ɓatawa a wajan aiki domin su sami damar zuwa su dinga yin wasu abubuwan da za su dinga samin ƙarin kuɗaɗen kashewa.
