News
Rikicin Sudan: Sama da mutane dubu 20 suka tsallaka zuwa Chadi
DAGA YADIR SANI ABDULLAHI
Hukumar abinci ta duniya ta ce hukumomin Chadi hade da kungiyoyin agaji na bukatar tallafin gaggawa domin taimakawa dubban masu gudun hijira dake tsallakawa daga sudan dake makotaka da kasar.
Majalisar dinkin duniya ta ce akalla mutane dubu 20 ne suka tsallaka Sudan zuwa Chadi tun bayan barkewar rikici tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun kai daukin gaggawa a farkon watan nan na Afrilu.
Darektan hukumar a Chadi, Pierre Honnorat na cewa bukatar ta yi tsanani sosai domin nan da makonni 6 ko 8 masu zuwa ba za su iya kai wa yankunan da masu gudun hijirar suke dauki ba saboda yanayi na ruwan sama.
Tun a farkon makon nan aka soma rabawa ‘yan gudun hijiran da suka isa kan iyakar Adre abinci da sauran kayakin jinkai.
Rikicin da aka shafe sama da makonni 2 ana yi ya mayar da Khartoum tamkar filin daga, sannan ya jefa illahirin Kasar cikin halin kaka-ni-kayi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
