News
Sudan:Karin ‘yan Najeriya Sama Da 1,000 sun bar birnin Khartoum
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu ‘yan Najeriya 1,350 a ranar Lahadin da ta gabata sun bar birnin Khartoum na Sudan da yaki ya daidaita zuwa Port Sudan inda za a dawo da su ta jirgin sama zuwa gida. Kamar yadda jaridar Nation ta ruwaito.
Port Sudan wani birni ne na Sudan mai tazarar kilomita 825 daga birnin Khartoum, inda har yanzu jirage za su iya sauka da tashi duk kuwa da yakin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces (RSF), karkashin jagorancin wasu janar-janar din soji guda biyu a rikicin neman mulkin kasar.
Rikicin Sudan: Sama da mutane dubu 20 suka tsallaka zuwa Chadi
Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar amfani da Port Sudan ne saboda matsalolin da rukunin farko na ‘yan Najeriya 637 suka fuskanta a kan iyakar Sudan da Masar.
Kashi na farko na mutanen da aka kwashe ana dawowa da su gida daga Alkahira babban birnin Masar.
Shugabar Hukumar Kula da Kasashen Waje ta Najeriya (NIDCOM) Misis Abike Dabiri-Erewa, a jiya ta tabbatar da jigilar rukuni na biyu na ‘yan Najeriya daga Khartoum.
Bayan an ba da izini, za a kwaso wadanda ke kan iyaka da Masar zuwa Najeriya daga filin jirgin saman Abu Simbel da jirgin saman Najeriya Air Force C-130.
