Connect with us

News

Yar Najeriyar da ta shafe awa 88 tana girki babu ƙaƙƙutawa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Gwamnar girki a Najeriya, Hilda Effiong Bassey, da aka fi sani da Hilda Baci ta kafa tarihin girki a duniya, bayan shafe tsawon sa’o’i 87 da mintuna 50 tana girke a tsaye.

Advertisement

Hilda mai shekara 27, ta shafe wuni hudu tana girke domin kafa tarihin zarta Lata Tondon ta Indiya da ta shiga kundin tarihin bajinta na Guinness World Record.

Lata a 2019 ta shiga kundin Guinness bayan shafe sa’o’i 87 da minti 45 tana girki a tsakiyar Indiya.

Advertisement

Wani Mutum Ya Kashe Mahaifiyarsa Kan Naira 10,000

Bajintar da Hilda ta nuna a yanzu ya zarta na Lata, sai dai a hukumance ba a sanar da shigar da ita kundin Guinness ba.

Lata ta shaidawa BBC cewa ta yi wannan kokari ne domin karfafa gwiwar matasa.

Advertisement

Burin Hilda na kafa tarihi ya samu goyon-baya da yabo a shafukan sada zumunta. An yi ta wallafata da nuna girkin nata kai-tsaye a shafukan sada zumunta, wanda milyoyi musamman a Instagram suka kalla.

An gudanar da gasar girkin ne a birnin Legas.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending