News
Ƙabilar Bodi: Iya Girman Tumbinka Iya Farin Jininka
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A tsarin ƙabilar Bodi da ke ƙasar Habasha, mazaje masu ƙaton tumbi su ne waɗanda mata suka fi rububi kuma suka fi so da ƙauna.
Girman tumbinka, shi ne yake nuna irin farin jininka a tsakanin ƴan matan garin.
Kotu ta yankewa mutum uku hukuncin kisa kan satar waya da kamfuta
Su na gauraya jini da madara, sannan su sha domin ƙara ƙiba da kuma ƙara girman tumbin nasu.
Ƴan Wannan ƙabila ta Bodi, su na zaune ne a wani ɗan ƙaramin tsibiri da ake kira da ‘Omo’ a ƙasar ta Habasha, kuma su na matuƙar alfahari da wannan al’ada tasu ta rainon tumbi.
Advertisements
