News
Jami’in hukumar EFCC Ya Mutu A Wurin Fada Da Abokan Aikinsa
Wani jami’in Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ya rasa ransa a wani fada da ya barke tsakaninsa a abokan aikinsa a Jihar Sakkwato.
Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana cewa wasu jami’an hukumar gudu uku sun kaure da fada ne bayan takkada ta ta barke tsakaninsu a kan ajiyar wasu kaya.
Kotu ta yankewa mutum uku hukuncin kisa kan satar waya da kamfuta
Ya ce likitoci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato ne suka tabbatar da rasuwar jami’in mai suna Sufeto Abel Isah Dickson a ranar 7 ga watan Mayu da muke ciki.
Da yake sanar da hakan a safiyar Talata, Uwujaren ya ce sauran mutum biyun na tsare a hannun ‘an sanda, bayan aukuwar lamarin a ranar 5 ga watan Mayun da muke ciki.
Advertisements
