Politics
Doguwa da wasu Jiga-Jigan APC 2 Sun Hakura da takararsa ta neman zama Shugaban Majalisar Wakilai.
DAGA KABIRU BASIRU FULTAN
Shugaban Masu Rinjiya a Majalisar Wakilai, Hon. Alasan Ado Doguwa ya sanar da janyewa daga takararsa ta neman zama Shugaban Majalisar Wakilai.
Jaridar Politics Digest ta wallafa cewa Doguwan ya bayyana cewa yana tare da zabin da Uwar Jam’iyyar APC tayi na Abbas da Kalu a matsayin Shugaba da Mataimaki.
Doguwa ya jagoranci wasu ‘yan takara biyu Abubakar Makki da Tunji Oluwuyi da suka janye daga takarar a ranar Laraba.
A baya dai Doguwa ya bi sahun wasu masu neman kafa kawance don kalubalantar Abbas.
Advertisements
