Connect with us

News

Keyamo yace Muƙamin ƙaramin minista ya saɓa wa tsarin mulkin Najeriya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Karamin ministan kwadago da ayyuka, na Najeriya mai barin-gado, Festus Keyamo (SAN), ya gaya wa Shugaba Muhammadu Buhari mai barin-gado cewa nada mukamin karamin minista ya saba wa tsarin mulkin kasar.

Keyamo wanda babban lauya ne a Najeriya ya fadi hakan ne a jiya Laraba, lokacin da yake gabatar da jawabinsa a zaman majalisar zartarwa na ban-kwana domin kawo karshen majalisar, wanda Shugaba Buhari ya jagoranta a Abuja.

An Dage Fara Jigilar Maniyatan Kano Zuwa Kasar mai tsarki 2023

Karamin ministan ya nuna cewa wannan mukami da ake bai wa mutane yawanci da sunan gwamnatin hadin kan kasa kusan ba ya aiki a zahiri ga yawancin wadanda ake nadawa a matsayin.

Domin ba wani iko na a-zo-a-gani da suke da shi lamarin da a wani lokacin ma yake hada su rigima da wanda yake matsayin ainahin matsayin ministan.

Ya ce yawancin wadanda gwamnatocin baya suka nada wa a wannan mukami sun ki fitowa su yi magana ne saboda kar a ga ba su gode wa Shugabannin kasar da suka ba su mukamin ba.

Advertisement

Festus Keyamo shi ne kakakin rusasshen kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Tinubu da Shettima.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending