Connect with us

News

Jami’an Tsaro Na Farautar Masu Sayen Wayoyin Sata A Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Jami’an hukumar tsaro dake bada kariya ga fararen hula  Civil Defence reshen jihar Kano sunyi nasarar kama  wasu mutane biyar da ake zargin barayin waya ne.

Kamar yadda wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Ibrahim Abdullahi ya fitar a ranar Laraba, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Talata a unguwar SabonGari da ke karamar hukumar Fagge.

Keyamo yace Muƙamin ƙaramin minista ya saɓa wa tsarin mulkin Najeriya

Wadanda ake zargin sun hada da Faisal Usman mai shekaru 28 da Mansur Isa mai shekaru 38 da Abdullahi Bashir mai shekaru 25 da Ahmed Ibrahim mai shekaru 21 da Zulkifil Bello mai shekaru 25.

Sanarwar ta ce rundunar tana bin diddigin  abokan aikinsu, Sunday da Abdullahi, wadanda suka saba sayarwa da wayoyi da layukan waya..

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending