News
Firaministan kasar Indiya ya ci alwashin hukunta masu sakaci a haɗarin jiragen ƙasa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Firaministan kasar Indiya Narendra Modi ya ci alwashin ɗaukar tsattsauran mataki kan waɗanda aka samu da sakaci a hatsarin jirgin da ya afku a Jihar Odisha.
Jami’an hukumar kula da sufirin jiragen ƙasa sun ce mutum ɗari biyu da tamanin da takwas ne suka mutu kuma wasu kusan 1,000 suka jikkata a hatsarin, wanda ya haɗa da jiragen fasinja biyu.
Rahotannin farko-farko sun nuna cewa matsalar sadarwa ce ta haddasa hatsarin.
Shugaba Modi ya bayyana hatsarin a matsayin “mai sosa rai” bayan ya ziyarci wurin da kuma wadanda ke asibiti.
Rahotannin farko-farko sun nuna cewa matsalar sadarwa ce ta haddasa hatsarin.
Shugaba Modi ya bayyana hatsarin a matsayin “mai sosa rai” bayan ya ziyarci wurin da kuma wadanda ke asibiti.
Advertisements